1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bashar al-Assad tazarce cikin yaki

Abdoulaye Mamane Amadou
May 26, 2021

Al'umma a kasar Siriya na kada kuri'a a zaben shugaban kasa a wannan Laraba. Daga cikin 'yan takara uku da ke neman shugabancin kasar har da shugaba Bashar al-Assad da ke neman karin wa'adi na hudu a karagar mulki.

https://p.dw.com/p/3txJu
Syrien l Facebook von Al-Assad l Präsident Bahar Al-Assad im Kabinett
Hoto: Syrien Presidency Facebook Page/AFP

Bayan shafe shekaru 20 kan karagar mulki, shugaba Bashar al-Assad na daga cikin 'yan takara masu neman shugabancin Siriya, a yayin da zai fafata da wasu abokan hamayyarsa biyu. 

Sai dai tun ba a je ko ina ba kasashen yamma sun yi fatali da tsarin zaben, tare da bayyana shi a matsayin wata dama da shugaba Al-Assad yake nema ta ci gaba da dauwama kan madafan iko, duk da yakin basasar da ya daidaita kasar.

Fiye da mutum dubu 350 ne suka halaka sakamakon yakin basasar Siriya, a yayin da wasu miliyoyi suka kauracewa gidajensu domin samun mafaka a kasashen ketare.