Basirar 'yan Afirka kan yaki da cutar Corona
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yaba wa 'yan Afirka kan kirkiro hanyoyin yaki da cutar corona a nahiyar. Ga misalin irin kirkira na ceton rai.
Abin shakar numfashi da aka yi a gida
A birnin Nairobi na Kenya, dalibai masu koyon aikin likita a Jami'ar Kenyatta sun kirkiro na'ura mai kwakwalwa da ke dauke abin da ke taimakon maras lafiya numfashi. Masu bincike a kasashen Afirka suna neman hanyar samun abin da ke taimaka wa numfashi da man goge hannu (sanitizer) sakamakon karuwar bukata a duniya daga kasashe kamar Amirka.
Mafita mai arha
Vincent Ssembatya, Farfesa a Jami'ar Makerere da ke birnin Kampala na kasar Yuganda, ya kirkiro na'urorin taimakon numfashi masu arha domin taimakon tsarin lafiyar kasar da ke da karancin kudi. Ya hada kai da mai kera mototin Kiira. Ya bayyana dalilin "Kowa na bukatar na'urar, haka ya saka damar Afirka na samu kalilan ne."
Senegal ta zama cibiyar kirkira
Dalibai masu karanta fannin injiniya a Senegal sun hada kai da gwamnati wajen yaki da annobar corona: Gianna Andjembe yana babban digiri kan fannin injiniyan laturoni ya nuna yadda za a samar da na'ura mai sarrafa kanta ta man goge hannu da ya kirkiro. Daliban suna amfani da fasaha wajen rage tumbatsa a asibitoci.
Dr. Car na duba marasa lafiya
Wannan karamar na'ura mai suna Dr Car, daliban Senegal suka kirkiro. Tana gwada jini da zafin jikin marasa lafiya da ke dauke da corona. Likitoci suna amfani da Dr Car wajen duba marasa lafiya ba tare da kasada ba. Hatta mutanen yankunan karkara ana iya kai wa gare su ta wannan hanyar.
Maganin dauke wuta
A kasar Habasha matashi mai kirkira Ezedin ya kirkiro na'urar taimakon numfashi da mashin da ke dauke da man goge hannu ba tare da an taba jiki ba. Tuni aka fara aiki da abubuwa 13 daga cikin 20 da ya kirkiro. Ana saka sabulu a mashin na wannan hannun da ake takawa yake da na'ura mai kwakwalwa da ke aiki ko an dauke wuta.
Amfani da launin fasahar zane
Babu iyaka ga kirkire-kirkire a Afirka. Daga birnin Legas zuwa Nairobi, masu zane-zane na yi kan katanga da gidaje da ke tunatar da mutane muhimmancin ba da tazara, wanke hannu da kyallen rufe baki da hanci. Ana samun irin wannan aiki har a unguwar talakawa ta Kibera da ke Nairobi na Kenya.
Salon kitson corona
Mutane suna tuna wa kansu: Ta hanyar yin salon kitson corona da ba da tazara gami da amfani da kyallen rufe baki da hanci. Sannan suna wanke hannu domin kare kansu, a cewar mai kirkira Mable Etambo a unguwar Kibera da ke Nairobi na Kenya. Suna amfani da launika irin na kwayar cutar.
Abinci mai gina jiki har gida
Dokokin hana fita da aka kakaba sun tsauwala wa mutane wajen neman abinci. A birnin Harare na kasar Zimbabuwe an kirkiro fasaha ta sayar da abinci daga manoma zuwa gidaje. Kamfani yana amfani da mashin mai taya uku da tabbatar da tazara, kuma za ka iya sayan kyallen rufe baki da hanci.
Musanyen ilimi lokacin zaman gida
Rufe makarantu a daukacin kasashen Afirka ya hana koyarwa. Ana neman mafita: Misali a Tanzaniya an kirkirro wata manhaja da dalibai za su yi aikin da ita. An ci gaba da aikin da wannan fasaha har bayan sake komawa harkokin rayuwa.
Gano annoba
Ko'ina, kafofin sada zumunta da zamani sun zama hanyar yaki da corona. A Najeriya da Ghana an kirkiro wata manhaja ta COVID-19 da za ta taimaka wajen gano kasadar kamuwa da corona. Yayin da gwamnatin Afirka ta Kudu ke amfani da manhaja ta WhatsApp da ke ba da amba kan COVID-19. Sannan tsaffin dalibai a Cape Town sun kirkiro manhajar gano labaran karya da ake yadawa.