1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shigar Ukraine cikin NATO da saura - Jamus

April 21, 2023

Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius ya ce ya yi wuri a tattauna batun shigar da Ukraine cikin kungiyar tsaro ta NATO a wannan lokaci. NATO dai za ta yi taron a watan Yuli.

https://p.dw.com/p/4QNrc
Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine, ya yi kira ga kungiyar tsaro ta NATO da ta bude wa kasar kofar zama mamba a cikinta, a taronta na gaba da za a yi a cikin watan Yulin wannan shekara.

Shugaban na Ukraine ya yi kiran ne lokacin da Sakatare na kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya ziyarci kasar a karon farko tun bayan mamayar Rasha.

Mr. Stoltenberg din ya ce Ukraine na da damar shiga kungiyar, kuma batun tsaronta zai kasance cikin jerin manyan batutuwan da taron NATO na gaba zai mai da hankali a kai.

Sai dai kuma da yammacin jiya Alhamis ne ministan tsaron Jamus Boris Pistorius, ba a wannan lokaci ne ya kamata Ukraine ta shiga cikin kungiyar ta kawancen kasashen yammacin duniya ba.