1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron BRICS a Cape Town

Zainab Mohammed Abubakar
June 2, 2023

Afirka ta Kudu ta yi yunkurin kawar da kai daga matsayinta game da rikicin Ukraine, yayin da ta karbi bakuncin taron kasasahe masu samun bunkasar tattalin arziki wato BRICS.

https://p.dw.com/p/4S7cK
Südafrika Treffen der BRICS-Außenminister in Kapstadt
Ministocin harkokin wajen kungiyar BRICSHoto: Foreign Ministry Press Service/ITAR-TASS/IMAGO

Manyan jami'an diflomasiyya na Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu na ganawa a birnin Cape Town a rana ta biyu na tattaunawa kan aniyar kungiyar na samar da wata hanyar da za ta maye gurbin tsarin kasuwanci da kasashen yammacin duniya ke jagoranta.

Sai dai batun ko Putin zai halarci taron kungiyar da za a yi a watan Agusta, wanda aka gayyace shi kafin a ba da sammacin kama shi a ICC, ya mamaye taron na wannan makon. Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa na neman Putin kan zargin Rasha na korar yaran Ukraine ba bisa ka'ida ba.

Wani memba na kotun ICC da ke da huldar kasuwanci da tattalin arziki mai karfi da Amurka da Turai, ya ce ana sa ran Afirka ta Kudu ta kama shugaban na Rasha da zarar ya taka kafarsa a kasar.