Bayern Munich: Shugaba Uli Hoeness ya yi murabus
Kimanin shekaru 50 bayan da ya fara yin wasa a kungiyar, aikin Uli Hoeness a Bayern Munich ya zo karshe. Shugaban ya ce ba zai tsaya takarar sabon wa'adi a kungiyar da ta fi kowace lashe kofuna a Jamus.
Yin murabus
Dangantakar da ta faro a shekara ta 1974 bayan da Bayern Munich ta sanya hannu da dan shekaru 18 daga TSG Ulm 1846 ta kawo karshe. Uli Hoeness ya ce ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kungiyar ba. Ya cimma guda daga cikin wa'adi mai cike da nasarori a tarihin kwallon kafar Jamus. Tsohon shugaban Adidas, Herbert Hainer guda daga cikin shugabannin kungiyar zakarun na Jamus ne zai maye gurbin.
Maciyin kwallo
Tsawon lokaci kafin zama shugaba, Hoeness ya kasance dan wasan gaba, kana guda daga cikin 'yan wasan kungiyar Bayern da suka lashe kofin Bundesliga da na Turai har sau uku. Da yake wasa a yammacin Jamus, ya lashe kofin zakarun Turai da kofin duniya. A wasu shekaru, Hoeness da Gerd Müller sun kasance 'yan wasan gaba da Turai ke ji da su. Sai dai bai jima yana wasa ba, ya samu ciwo a gwiwarsa.
Manaja mafi karancin shekaru
Da ya gaza komawa filin daga sakamakon rauni, yayin da aka dauki aronsa a Nuremberg, Hoeness ya ajiye takalmansa na kwallo. Ya zama manajan Bundesliga mafi karancin shekaru a ranar daya ga watan Mayun 1979, yana da shekaru 27. Nan shi ne da shugaban Bayern a wancan lokaci Willi Hoffmann (daga hagu) kwana uku da kama aikinsa. Nasararsa ta farko a matsayin manaja da ci uku da daya a Darmstadt.
Mai baiwar kasuwanci
Kafin Hoeness ya zama manaja, ya cimma yarjejeniya da kamfanin kera manyan motoci na Magirus-Deutz domin daukar nauyin rigar 'yan wasan Bayern. Kudin ya bai wa Bayern damar dawo da dan wasanta Paul Breitner daga Braunschweig ta yammacin Jamus a 1978. Nan Breitner ne ke daga kambun Bundesliga da Bayern ta lashe a 1981. Sun samu sabani, bayan da Breitner ya soki lamirin shugabancin Bayern.
Mai rabon ganin badi
A ranar 17 ga watan Fabarairun 1982, Uli Hoeness ne kawai ya tsira a wani hadarin karamin jirgin sama, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa yammacin Jamus domin halartar wasan sada zumunci da kungiyarsa za ta fafata. sauran mutane uku da ke cikin jirgin sun mutu. Hoeness na yin kwana a lokacin da jirgin ya fadi, ba zai iya tuna komai a kai ba.
Mai kamfanin HoWe Sausage
Hoeness da ke zaman dan mahauta, ya samar da kamfanin HoWe sausage a birnin Nuremberg a shekara ta 1985, da a yanzu ke raba Sausage din ga manyan shaguna irin su Aldi da McDonalds. HoWe,da Hoeness ke samun mafi yawan kudin shigarasa, a yanzu dansa Florian ya karbi jagorancinsa.
Daga manaja zuwa shugaba
Bayan shekaru 30 a matsayin janaral manaja, a ranar 27 ga watan Nuwanbar 2009, Uli Hoeness ya samu matsayi mafi girma a Bayern Munich, inda ya lashe zaben shugaba a yayin babban taron kungiyar na shekara-shekara. Nasarori za su biyo baya, tun daga farkon kakar wasanni ta 2012 zuwa 2013 zuwa yanzu, Bayern ta dauki kambun Bundesliga sau shida a jere.
Shiga cece-kuce
Hoeness ya bayyana gabarsa karara ga tsohon mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Cologne da Bayer Leverkusen Christoph Daum. A yayin wata tattaunawa kan wasanni a gidan talabijin, ya bayyana zargin da ake wa Daum da ke shirin zama mai horas da 'yan wasan kwallon kafar Jamus a shekara ta 2000 na amfani da hodar iblis. An samu alamun hodar iblis a gashin Daum bayan da aka yi masa gwaji.
Babban mai nasara
Uli Hoeness ya lashe azurfa a matsayinsa na dan wasa, sai dai ya lashe kambu mai yawa a matsayinsa na shugaba.A shekara ta 2013, Bayern Munich ta lashe kambun treble; bayan da ta lashe kofin gasar Bundesliga da kofin Jamus da kuma gasar zakarun Turai a kaka guda. "Shekara mai ban mamaki," a cewar shugaban kungiyar da ke walawa, duk kuwa da sammacin da aka aika masa kan kin biyan haraji.
Faduwa kasa
A ranar 13 ga watan Maris na 2014: An kama Hoeness da laifin kin biyan haraji da yawansa ya kai Euro miliyan 28 da dubu 500, kwatankwacin dalar Amirka miliyan 32, inda aka yanke masa hukuncin shekaru uku da rabi a gidan kaso. Hoeness ya shiga gidan kaso a ranar biyu ga watan Yunin 2014, abin da ya sanya darajar shahararre kuma fitaccen dan wasan Jamus faduwa kasa.
Sake zama shugaba
Kwana guda bayan yanke masa hukunci, Uli Hoeness ya yi murabus a matsayin shugaban Bayern. Sai dai ya sake dawowa bayan shekaru biyu da rabi, inda ya lashe zabe yayin taron kungiyar na shekara-shekara a ranar 25 ga watan Nuwambar 2016. Shi ne dan takara na farko da ya amince ba zai sake tsayawa takara ba tun farkon shekara, bayan Karl Hopfner shugaban kungiyar a lokacin da Hoeness ke kurkuku.
Mai taimako
Ko yaushe Hoeness na kawo dauki ga wani nasa da ke bukatar taimako. Kungiyoyi kamar St. Pauli har ma manyan abokan hamayarsu Borussia Dortmund sun ci gajiyar mutuntakarsa. Kullum yana taimaka wa tsofaffin abokansa irin su Gerd Müller da ke fama da shan giya da 'yan wasa kamar Sebastian Deisler da ke fama da kasala da kuma Dietmar Hamman wanda matsalar shan giya da cacaca suka zame masa jiki.
Mai son iyalinsa
Kusan ko yashue, Uli Hoeness na asirta abin da ya shafi rayuwarsa ta gida. Ya auri matarsa Susanne sama da shekaru 40 din da suka gabata. Yaransa Sabine da Florian sun girma. Hoeness na jin dadin rayuwa a tsanake a gida kuma ba a taba jin wani cece-kuce dangane da iyalansa ba.