Daga cikin batutuwan da Labarin Wasannin na wannan karo ya kunsa za ku ji yadda bayan wasanni mako na uku na kakar wasannin Bundesliga ta shekarar bana kungiyar Bayern Münich ke ci gaba da yin kane-kane a saman tebirin na Bundesliga bayan da a karshen mako ta lallasa Bayer Leverkusen da ci uku da daya a wasan da suka kara a filin wasa na Allianz Arena na birnin Münich.