1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Nijar ta kori karar wasu 'yan adawa

Lawan Boukar AH
December 3, 2020

Mutane guda biyar ne na jam'iyyar Modem Lumana Africa suka shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar takarar Mohamed Bazoum a zaben shugaban kasa wanda suka ce ba dan kasa ne ba.

https://p.dw.com/p/3mBWF
Niger 's Innenminister Mohamed Bazoum
Hoto: Getty Images/K. Tribouillard

A karo na uku jere ke'nan da kotun ta Diffa take saka ranar yin shari'a a kan zargin tana dagewa, a karshe bayan zaman ta na uku kotu ta yi watsi da karar da magoya bayan jam'iyyar ta Lumana suka shigar. Wannan hukunci dai da kotun ta yanke ya kawo karshen ce-ce-ku-ce da aka dade ana yi a kasar a game da takarar ta  Mohamed Bazoum a zaben shugaban kasar da za a yi a cikin watan Disamba.Tun farko kotun tsarin milkin ta tabbatar da takarar ta Bazoum tare da soke ta daya daga cikin babban abokin hamayar sa Hama Amadou. An shirya gudanar da zaben shugaban kasar ne na Nijar a ranar 27 ga watan Disamba sai dai har ya zuwa yanzu akwai rashin zutuwa tsakanin gwamnatin da 'yan adawar a sakamakon soke takarar jagoran 'yan adawar Hama Amadou. Yanzu haka dai kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka Ecowas na kokarin shiga tsakanin domin ganin an samu fahimtar juna kafin zaben tsakanin gwamnatin da 'yan adawa. Tuni dai da aka bude yakin neman zabe na kananan hukumomi tun ranar Larba da misalin karfe sha biyu na dare.