1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Belarus ta rufe iyakarta da Ukraine

Abdul-raheem Hassan
July 3, 2021

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya killace iyakar kasarsa da Ukraine, saboda zargin ana shigo da manyan makamai ta kan iyakar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3vyMC
Bitte nicht verwenden NUR für den Belarus Special des Investigativ-Teams, Sandra Petersmann
Hoto: State TV and Radio Company of Belarus via AP/picture alliance

Shugaba Lukashenko ya ce jami'an tsaro sun bankado wasu muggan kwayoyin maye da ke taimakawa 'yan ta'adda, ya kuma ce kwayoyin suna da alaka da kasashen Jamus da Ukraine da Amirka da Poland da kuma kasar Lithuania.

Lukashenko ya ce yana zargin wadannan kasashe da shirya makarkashiyar kifar da gwamnatinsa da karfin tuwo, sai dai ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce yanzu ba lokacin yin martani ba ne kan wannan zargi na Lukashenko.