Belin masu zanga-zanga a Masar
December 4, 2013Talla
Wata kotu a kasar Masar ta bada belin wasu masu zanga-zanga su 23 da aka kame a makon da ya gabata, bisa zarginsu da aiwatar da zanga-zanga ba tare da izini ba.
A ranar 26 ga watan Nuwamban da ya gabata ne dai, suka gudanar da haramtacciyar zanga-zanga da aka bayyana a matsayin karo na farko, kwanaki biyu bayan da shugaban kasar na wucin gadi Adly Mansour, ya sanar da dokar haramata zanga-zanga a kasar.
Tun dai bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin hambararren zababben shugaban kasar ta Masar Mohamed Morsi, ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a kasar, yayin da a hannu guda kuma jami'an tsaro ke kokarin dakile zanga-zangar da karfin tuwo.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba