1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljiyam ta mika Abdeslam ga Faransa

Mohammad Nasiru AwalApril 27, 2016

Hukumomin kasar Beljiyam sun mika mutumin da ake zargi da hannu a harin ta'addanci birnin Paris Salah Abdeslam ga mahukuntan kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/1IdYB
Salah Abdeslam Fahndungsfoto
Hoto: Police Federale Belgien

A wannan Larabar kasar Beljiyam ta tasa keyar Salah Abdeslam da aka yi imani shi ne ya tsira da ransa daga cikin 'yan ta'addan da suka kai hari a birnin Paris cikin watan Nuwamban bara da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 130, zuwa kasar Faransa domin ya fuskanci shari'a. Abdeslam dan shekaru 26 ya kasance wanda aka fi nema ruwa a jallo a Turai gabanin a cafke shi a birnin Brussels ranar 18 ga watan Maris, bayan an kwashe watanni hudu ana farautarsa. An dauke shi da jirgin sama mai saukar ungulu zuwa Paris cikin tsauraran matakan tsaro. Ministan shari'ar Faransa Jean-Jacques Urvoas ya ce za a tsare Abdeslam a wani kurkuku mai cikakken tsaro da ke a yankin birnin Paris. Franck Berton shi ne lauyan Faransa da ke kare Abdeslam.

"Dole ne a kare wannan matashin. Dole ne a ba shi damar yin bayani dangane da abin da ya yi da wanda bai yi ba. Ba muna wakiltarsa ba ne a matsayin wanda aka shafa wa kashin kaji domin shi kadai ya saura daga hare-haren na Paris."