1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benazir Bhutto ta koma gida Pakistan

October 18, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8G

Bayan shekaru 8 na gudun hijira tsohuwar FM Pakistan Benazir Bhutto ta koma gida. Dubun dubatan magoya bayanta suka yi mata gagarumar tarba lokacin da ta isa birnin Karachi dake kudancin Pakistan. A girke dubban jami´an tsaro bayan barazanar da ´yan kungiyar al-Qaida suka yi na halaka ta. Bhutto ta ce ta koma gida ne dauke da wani sako na sauyi da kuma fatan inganta makomar mulkin demokiradiya a cikin kasar.