'Yan kasuwar Nijar na martani ga Benin
February 29, 2024Cikin wata sanarwa da Hukumar Hana Fasa-kwabri ta Benin din ta wallafa a watan da ya gabata ne dai, ta sanar da wannan mataki na shirin fara gwanjon wasu hajojin 'yan kasuwar Nijar din da ta ce sun cika wa'adin zamansu a tashar jiragen ruwa ta Cotonou. Matakan dai sun hadar da shirin kadawa wasu daga cikin kayan 'yan kasuwar Nijar da ke makale a tashar jiragen ruwan Cotonou sakamakon takunkumin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da ya biyo bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023 kararrawa, abin da ya sa kungiyoyin 'yan kasuwar yin kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin kare dukiyarsu da ke Benin din. Yanzu haka dai al'umma ta zuba ido domin ganin matakin da hukumomin mulkin sojan Nijar za su dauka kan wannan matsala ta 'yan kasuwa da makwabciyar kasa Benin, wadda har yanzu kan iyakarta da Nijar din ke ci gaba da kasancewa a rufe bayan da gwamnatin Yamai din ta umurci hakan duk da dage takunkumin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi wa Nijar din.