1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bhutto ta lashi takobin ci-gaba da zama a Pakistan

October 20, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8A

Tsohuwar FM Pakistan Benazir Bhutto ta ce daya daga cikin kungiyoyin ´yan ta´adda 4 ciki har da Taliban da al-Qaida ke da hannu a yunkurin halaka ta da bai yi nasara ba. Bhutto ta kuma nuna bukatar gudanar da bincike akan dalilan da suka sa aka kashe fitilun kan hanyar da jerin motocin ta suka bi. Bhutto ta fadawa wani taron amnema labarai a birnin Karachi cewa fashewar bama-baman ba harin ne akan ba a´a hari ne akan demokiradiya da kuma hadin kan al´umar kasar Pakistan. Jam´iyar ta ta Pakistan People´s Party ta ce Bhutto zata ci-gaba da zama cikin kasar kuma zata shiga cikin zaben ´yan majalisar dokoki dake tafe a kasar duk da mummunan harin. Sama da mutane 130 suka rasu sannan kimanin 250 suka jikta lokacin da wasu bama-bamai biyu suka fashe a kusa da wata babbar mota dake dauke da Bhutto. Kasashen duniya dai sun yi tir da wannan hari.