1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya bayyana manufofinsa na ketare

February 5, 2021

Shugaba Joe Biden ya sanar da kawo karshen tsoma baki da Amirka ke yi a matakan soji a kasar Yemen, inda kasar Saudiyya ta shafe shekaru tana yaki da ‘yan-tawayen Houthi, lamarin da ya yi sanadin kashe dubban rayuka. 

https://p.dw.com/p/3owGD
Washington Außenministerium Rede USA Außenpolitik Biden
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

“Amirka ta sake kunno kai, diflomasiyya ta farfado Wannan shi ne taken babban jawabin da Shugaba Joe Biden ya yi a ranar Alhamis (04.02.2021) da maraice a ma’aikatar harkokin waje da ke birnin Washington DC, wanda shi ne na farko kan manufofin gwamnatinsa inda ya ci gaba da warware wasu manufofin gwamnatin Trump, Shugaban ya yi kashedi ga abokan hamayya da masu mulkin danniya, sannan ya jaddada mahimmanci kawance wajen cimma wasu muradu kamar su; Kare ‘yanci, bai wa jama’a dama, kare hakkin dan-Adam da kuma bin dokoki.

Bildkombo Angela Merkel und Joe Biden
Biden ya yi alkawrin daidaita dangantaka da Jamus


Amirka za ta ci gaba da jibge soji a Jamus

Sauran mahimman manufofin da Biden ya zayyana da suka sha bambam da na wanda ya gada sun hada da ci gaba da jibge sojojin Amirka a kasar Jamus, da  yin maraba lale da ‘yan gudun hijira dubu 125 a kowace shekara, daga dubu 15 kacal a zamanin mulkin Trump. Kazalika, Biden ya sake jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga masu auren jinsi daya ko ‘yan mata-maza a kasashen duniya baki daya. 


Shugaban na Amirka wanda ya ce za a iya dakile kalubalen da duniya take fuskanta a wannan zamani ne kawai, ta hanyar yin aiki tare tsakanin kasashe, ya gwasale tsarin mulkin danniya, sannan ya bukaci da a hamzarta sakin shugabannin farar hula na kasar Bama, da jigon adawar Rasha Alexei Navalny, yana mai aika sako kai tsaye ga Shugaba Putin na Rasha cewa, lokacin kawar da kai ya wuce. Ga kasar Sin kuma, Sai ya ce "Za mu tashi tsaye a kan cin-kashin da Sin take yi a harkar kasuwanci. Za kuma mu sa-idanu sosai a kan yadda take danne hakkin dan-Adam.

Ga ma’aikatan diflomasiyyar Amirkar kuwa, sabon Shugaba Biden ya ce,zai ba su goyon baya, su yi aikinsu, ba tare da yi masu bita-da-kulli ba, ko kuma saka siyasa cikin ayyukansu, sabanin tsegunguman da aka rika yi cewa, gwamnatin Trump ta kashe karsashin aikin wasunsu, inda ta rika zargin kamar ba sa tare da ita.

China | Präsident Xi Jinping und Joe Biden
Da alama Biden zai samun sabani da Chaina a kan kasuwanciHoto: Lintao Zhang/AP Images/picture alliance

Biden ya bayyana manufofinsa na ketare