1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya gana da ministocin Ukraine

March 26, 2022

Yayin da ake ci gaba da nemo hanyoyin kawo karshen yaki tsakanin Rasha da Ukraine, shugaba Joe Biden na Amurka ya gana da ministocin Ukraine biyu a birnin Warsaw a Poland.

https://p.dw.com/p/495AJ
Warschau US-Präsident Biden trifft Ukraine-Flüchtlinge
Hoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

Wannan dai na kasancewa karon farko da shugaba Biden ya gana da manyan jami'an Kyiv gaba-da-gaba tun bayan da Rasha ta fara mamaya a Ukraine. Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba da takwaransa na tsaro Oleksii Reznikov na fatan samun karin kwarin gwiwar yaki a wannan ganawar. 

Kuleba ya ce sun tattauna kan sabbin takunkuman da za a kakabawa Rasha da kuma yadda za ta dandana kudarta idan aka aiwatar da su yadda suka kamata.

An dai gudanar da tattaunawar ce tsakanin bangarorin biyu a kusa da filin jirgin kasa na birnin Warsaw, inda a nan ne ake samun kwararar 'yan gudun hijira da ke tserewa yakin Ukraine. Yayin da yake ganawa da 'yan gudun hijrarar, shugaba Biden ya baiyana shugaba Vladmir Putin na Rashar a matsayin "dan ina da kisa" ya na mai nuna rashin gamsuwa da ikrarin da Rasha ta yi na rage manufofin ci gaba da yaki.