1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya ki danganta Rasha da ta'addanci

Abdullahi Tanko Bala
September 7, 2022

Gwamnatin shugaba Joe Biden na Amirka ta ce ayyana Rasha a matsayin kasar da ke daukar nauyin ta'addanci ba zai amfanar da komai ba, a saboda haka ta yi watsi da bukatar Ukraine kan wannan mataki.

https://p.dw.com/p/4GVVz
USA Präsident Joe Biden
Hoto: Matt Slocum/AP Photo/picture alliance

Amirka ta ce ba ta da niyyar ayyana Rasha a matsayin kasar da ke dauyin ta'addanci. Shugaban majalisar tsaro ta Amirka John Kirby ya ce yin hakan ba shi ne mataki mafi dacewa na ganin Rasha ta girbi abin da ta shuka ba.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ne dai ya yi kira ga kasashen yamma su ayyana Rasha a hukumance a matsayin kasar da ke daukar nauyin ta'addanci sakamakon hare haren da suka hallaka fararen hula musamman a wani kantin sayar da kaya da ke Kremenchuk a watan Juni inda akalla mutane 18 suka rasu.

A waje guda hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci samar da tsaro da kariya a kusa da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhia wadda Rasha ta mamaye yayin da ake cigaba da luguden wuta a yankin.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Rasha da Ukraine su samar da wata da'ira da za a daina fada kusa da tashar makamashin nukiliyar ta Zaporizhia