Biden ya tattauna da shugabannin Turai
November 11, 2020Talla
Manyan shugabannin kasashen duniya aminan Amirka sun tattauna ta wayar da tarho da zababben shugaban kasar Joe Biden inda suka jaddada aniyarsu ta hada hannu domin aiki tare, duk kuwa da ikirarin da sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo yake yi na cewa shugaba Trump ne zai cigaba da jagorancin kasar.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta wayar tarho, ta bi sahun kasashen duniyar wajen taya Joe Biden murnar nasarar da ya samu.
Mai magana da yawun shugabar Steffen Seibert ya ce shuwagabannin guda biyu sun tattauna batun kawance tsakanin Turai da Amirikar.
Kasashe da dama na tarayyar Turai sun baiyana fatan kyautatuwar dangantaka tsakanin tarayyar Turai da Amirka a karkashin mulkin Joe Biden.