Bikin baje kolin hotuna
July 2, 2024A Jamhuriyar Nijar kungiyar raya al'adu ta kasar Jamus ta Goethe Institut, ta bude bikin baje kolin wasu hotuna. Makasudin shirin shi ne amfani da wadannan hotuna da wasu matasan kasashen Sahel da kungiyar ta Goethe Institut ta bai wa horo fasahar yin hoto suka dauka, domin fadakar da al'ummar girman matsalar gurbatar muhalli a kasashen yankin da kuma bukatar daukar matakan tsarkake shi.
Karin Bayani:
Matsalar sauyin yanayi da gurbatar muhalli na daga cikin matsalolin da ke yin illa ga rayuwar al'umma a kasashen Sahel da dama. Domin taimaka w aga fadakar da al'ummar yankin girman wannan matsala ce da bukatar daukar matakan tunkarar ta, kungiyar raya al'adu ta kasar Jamus ta Goethe institut, ta horas da wasu matasan kasashen Jamhuriyar Nijar, Mali Burkina Faso, moritaniya da Chadi fasahar daukar hotuna ta yadda ta hanyar hotunan za su iya jan hankali jama'a da kuma fadakar da su a game da girman wannan matsala ta gurbatar muhalli a kasashen na Sahel, matsalar da ke zama dalilin mafi yawancin matsaloli na tsaro da zamantakewa da ma tattalin arziki da ke addabar kasashen.
Tarin ‘yan kallo ne dai suka halarci bikin baje kolin hotunan wadanda ke nuna irin yadda shara leda da ruwan kwatami da sauran datti suka mamaye muhallin gidaje da unguwanni a garuruwa da dama na kasashen Yankin na Sahel. Shi ma dai jakadan Jamus a Nijar Mista Olivier Schnakenberg ya bayyana gamsuwarsa da wannan baje kolin na hotuna. Za a dai share tsawon mako daya ana gudanar da baje kolin hotuna na ankarar da al'umma Nijar girman matsalar gurbatar muhalli a Sahel, bikin da za a gudanar da irinsa a sauran kasashen na Sahel a nan gaba.