Bikin nuna hotuna: Afirka tsakanin rayuwar manyan birane da kauyuka
Ambaliyar jama'a da bunkasar birane - Sauyi cikin gaggawa a Afirka ya dauki hankalin masana al'adu. Bikin ya nuna hotunan Kelechi Amadi-Obi na mawaki Keziah Jones a birnin da shine mafi girma a Afirka kudu da Sahara.
Bikin nunin hotuna a birni mai cunkoso
Ambaliyar jama'a da bunkasar birane - Sauyi cikin gaggawa a Afirka ya dauki hankalin masana al'adu. Bikin ya nuna hotunan Kelechi Amadi-Obi na mawaki Keziah Jones a birnin da shine mafi girma a Afirka kudu da Sahara.
Birane masu bunkasa. Masu sana'ar daukar hoto dake bunkasa
A kawar da tsoho a sami sabo. Masu daukar hotuna fiye da 50 ne a Lagos suka nuna hotunansu kan canji da ake samu cikin gaggawa a manyan biranen Afirka. "bikin "nunin hotunan na Lagos" shi kadi ne na kasa da kasa a Najeriya inda maida burinsa game da hade masu sana'ar daukar hotuna daga ko ina cikin duniya.
Mai daukar hotuna matashi daga unguwar 'yan share-wuri-zauna
Afoso Sulayman bikin nunin hotuna na Lagos shine karon farko da ya sami damar nuna hotunansa. Ya fito ne daga Makoko, daya daga cikn manyan wuraren yan share wuri zauna a Lagos, kuma tuni yake mafarkin zama mai sana'ar daukar hoto. " Dan uwana ya bani labarin wani horo na daukar hotuna da aka yi a Maroko", inji Sulayman. Horon an fara shi ne da mutae 30, amma su biyu n suka ga karshensa.
"Kowa tasa ta fisshe shi"
Hotunan Sulayman musamman sun fi maida hankali ne ga yadda rayuwa take a unguwar Makoko. Rayuwar ta tattara ne ga yadda mutane 100.000 suke zaune suna rayuwarsu a wuri mai matatsi. "Rayuwar dai ta tattara ne ga gwagwarmayar neman tsira da samun dan kudin da zai bada damar ci gaba da rayuwa", inji Sulayman. Shima kansa yana cikinsu, saboda da daukar hoto kadai ba zai iya rayuwa ba.
Zaman makwabtaka
Sulayman yana ganin wata babbar dama ce gareshi saboda ya fito daga unguwar 'yan-share-wuri-zauna. Saboda haka ne yake daukar hotunan makwabtansa a matsayin abokan zama amma ba baki ba. " Da yawa suna taka tsan-tsan. Nakan ce masu rayuwar tana da kyau a duk lokacin da aka so jin yadda zamanmu yake. Da yawa sukan kuma gane abin da nake nufi".
Hotuna masu daura da rayuwar manyan birane
Patrick Willocq ya nuna hotunan da suka zama daura da wadanda ke nuna rayuwa a unguwannin 'yan share-wuri-zauna a manyan birane Willocq ya zauna watanni da dama a kauyukan Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango. "Burina shine in nuna yadda ake rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankunan karkara, saboda mafi yawan abinda muka fi ji shine labarin tashe-tashen hankula a gabashin Kwango.
Maida duniya gida daya ya shigarwa da kauyuka kayan roba
Willocq tun yana yaronsa ya zauna a Kwango. Hotonsa da yafi daukar hankali shine wanda ya nun yadda batun cudeni in cudeka tsakanin kasashen duniya ya kai ga kananan kauyuka, inda misali, kujerun roba suka zama wata alama ta jin dadin rayuwa. Ga Willocq, wannan dai ci gaba ne na mai hakar rijiya. "A zahiri kujerun da aka yisu da itace sun fi karfi, sun fi jure wahala, kuma sun fi dadin zama".
Rayuwar yau da kullum a Senegal
Mouhamadou Moustapha Sow ya gabatar da hotunan dake nuna adda rayuwar yau da kullum take a kasarsa Senegal. A hakika Sow masani ne a fannin zanawa da dinka tufafi, inda yake daukar hotuna idan yana da lokaci. "Burina shine in nuna yadda bunkasar rayuwa da yadda al'amura suke a birnin Dakar."
Ba a kallon Afirka da idanun basira
Ya zargi kafofin yada labarai na yamma da laifin yiwa Afirka kalon abubuwa marasa tushe. A hamadar kasar Mauretaniya, ci karo da wani tsohon akwatin talbijin, nan da nan ya kai ga tunanin yadda hotunan da zai dauka zasu zama."Hotuna zasu iya nuna wani dan karamin bangare ne kawai na yadda rayuwa tak a garuruwa. Wannan kua abin nake son nunawa da wannan tsohon akwatin Talbijin."