Bikin rufe gasar Rio 2016, cikin hotuna
An kammala gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympics ta bana da bukukuwa masu ban sha'awa, a filin wasa na Maracana da ke Brazil, duk da ruwan sama da kuma karancin 'yan kallo yayin rufe gasar.
Kammalawa ta birgewa
Za a iya cewa wasannin na birnin Rio sun fuskanci tataburza mai yawa, sai dai masu masaukin bakin, sun gudanar da bukukuwan kammala gasar mai birgewa.
Bukuwa na kasa
Sabanin lokacin bikin bude gasar, inda baki dayan 'yan wasan kowa kansa ya sani yayin da ya ya shiga filin wasana na Maracana, a bikin rufe gasar, 'yan wasan sun fita daga filin wasan na Maracana a suna masu nuna hadin kai da kaunar juna.
Mai rike tutar Jamus: Sebastian Brendel
Dan gasar tukin kwale-kwale da ya lashe kambun zinare biyu yayin gasar, an zabe shi ne ya jagoranci tawagar 'yan wasan Jamus yayin bikin rufe gasar.
Nau'in kaloli daban-daban a ko ina
Kamar yadda wasannin suka kasance, bikin rufe gasar bai bayar da kunya ba a ta fannin kayata awajen da nau'in kaloli daban-daban, an nuna 'yan Brazil daban-daban da suka yi fice a yayin rufe gasar.
Lokacin biki!
babau karancin kishin kasa a filin wasa na Maracana, yayin da aka kammala wasannin na Rio. Da yawa na ganin wannan wata dama ce ga kasar na nuna matsayin da take da shi a yanzu a duniya.
Iska mai karfi
Dare ne mai danshi da sanyi a birnin na Rio, sai dai ruwa da iska basu hana dubban mutanen su halarci filin wasan na Maracana ba.
Gare ka, birnin Tokyo
A karshen bikin rufe gasar, birnin Tokyo ya ba da kwarya-kwaryan haske kan abin da za a tsammata a gasar 2020, da za a gudanar a babban birnin kasar Japan.
Ba abin da aka manta sai gashin baki.....
Firaministan Japan Shinzo Abe ya yi shiga irin ta "Super Mario" dan wasannin na'urar Computer da ake kira da "video game" da nufin tallata gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsallen na birnin Tokyo da za a gudanar a shekara ta 2020. Amma kash sun manta su sanya masa gashin baki a yayin da suke yi masa shigar.