Bikin tunawa da hadewar Jamus kasa guda
October 3, 2014Birnin Hanover da ke arewacin kasar shi ne ya ke daukar bakuncin babban taron da ake yi inda daruruwan baki suka hadu tare da shugabar gwamnati Angela Merkel da kuma shugaban Jamus din Joachim Gauck don gudanar da addu'o'i.
A karon farko dai wakilan Yahudawan da ke nan Jamus da na mabiya addinin Islama sun hadu a waje guda da takwarorinsu da ke bin tafarkin addinin Kirista inda suka yi jawabai iri daban-daban wandanda galibinsu suka maida hankali wajen nuna alfanun zama lafiya.
Jawaban da aka yi har wa yau sun tabo irin halin da mutane ke ciki a yankunan da 'yan kungiyar nan ta IS ke rike da su a Iraki da Siriya tare da jinjina irin asarar rayukan bakin hauren da ake samu yayin da suke yunkurin tsallaka tekun meditereniyan a kokarinsu na shiga Turai.