Bin Salman ya bukaci tsagaita wuta a Gaza
March 11, 2024Yarima Muhammad Bin Salman ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen ta'asar da ake tafkawa a yankin zirin Gaza, a daidai lokacin da al'umma musulmi a Saudiyya da yankunan Falasdinawa da kuma wasu kasashen musulmi da dama suka wayi garin wannan Litinin da Azumin watan Ramadan.
Yariman na Saudiyya ya yi wannan kira ne a jawabinsa na sanar da ganin watan Ramadan da yammacin Lahadi, inda ya bukaci kasashen masu karfin fada a ji da su kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza tare da gaggauta samar da hanyoyin shigar da kayan agaji ga al'ummar yankin da ya fara fama da yunwa.
Karin bayani: Amurka ta aike da jirgin dakon kaya na ruwa dauke da kayan agaji Gaza
Har kawo wannan lokaci duk wani kokari na samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin na Gaza ya ci tura, hasali ma ko da a ranar Lahadi dakarun Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a dan karamin yankin na Falasdinu da ya fada yaki sama da watanni biyar da suka wuce.