Binciken kisa a boren daliban Nijar
May 3, 2017Daukacin manbobi kwamitin 13 mai kunshe da bangaren dalibai da ke da mambobi biyar da na gwamnatin Nijar da suma ke da manbobi biyar da kuma bangaren hukumar CNDH mai kula da kare hakin dan Adam da ke da mambobi biyu, yayin da hukumar kula da shiga tsakani CNDS ke da mamba guda dai, sun sha rantsuwar kama aiki. Babban nauyin da ya rataya a wuyan sabon kwamitin da ya karbi rantsuwa da Alkur'ani mai girma a gaban babar kotun daukaka karar dai shi ne: zakulo dalilan da suka kai ga aika-aikar kisan dalibi a ranar 10 ga watan MAris din da ya gabata, a babbar jami'ar Yamai inda wata arangamar da ta rutsa da dalibai da jami'an tsaro ta yi sanadiyar mutuwarsa tare kuma da raunata wasu daliban da dama. Lamarin dai ya afku ne a yayin wata zanga-zangar lumana da daliban suka kudiri aniyar gudanarwa. Malam Tsalha Kaila shi ne mataimakin magatakardan kungiyar daliban jami'ar birnin Niamey ta UENUN ya ce fatansu shi ne mambobin wannan kwamitin su gabatar da aikinsu tsakani da Allah amma idan har ba'a fito da gaskiya ba to za su dau matakai.
An dai rataya shugabancin kwamitin ne ga hukumar kare hakin dan Adam ta CNDH wacce shugabanta Farfesa Khalid Ikri zai jagoranta, kana kwamitin zai shafe tsawon kwanaki ya na nazari tare da bi sau da kafa tun daga inda lamarin ya taso har izuwa inda a ka tsaya. A hirarsa da tashar DW, babban sakataren ma'aikatar hukumar kare hakin dan Adam din mai shari'a Ali China Kourgeni ya yi kwamitin zai zartar da ayyukansa tun daga inda abin ya faru har zuwa karshe, kana bincikensu zai hada tun daga kan ministan ilimi da na 'yan sanda da daliban dama wuraren da akayi abubuwan gaba daya, domin ganin cewar an fito da gaskiya. Shugaban gwamnati Firaminista Brigi Rafini ne dai ya aika takardar kafa kwamitin domin cika daya daga cikin sharuddan da dalibai suka gindaya biyo, bayan hatsaniyar da ta barke tsakaninsu da jami'an tsaro wanda ya kai ga rufe wuraren daukar karatu a jami'o'in Yamai da Maradi, kana sakamakon binciken zai shiga ne ta hannun shugaban gwamnatin, kafin daga bisani akai ga wallafa shi ga jama'a, ko da yake har yanzu babu adadi na kwanaki ko makwannin da sabon kwamitin zai dauka domin gudanar da ayyukansa.