Birnin Kudus a da da yanzu
Birnin Kudus jigo ne babba a rikicin Isra'ila da Falasdinawa. Yaya birnin yake shekaru 50 baya a lokacin yakin kwanaki shida kuma me ne ne ya sauya tun daga wancan lokaci.
Tsaunin Zaitun a yau
'Yan yawon bude ido daga kan tsauni suna iya kallon tsohon garin Birnin Kudus. Dutsen wani yanki ne na tsaunukan arewa maso gabas da kuma gabashin masallacin Al-Aksa da tsohon garin kamar yadda ake iya gani a hoton. Tsohuwar katangar birnin da hasumiyar masallaci mai tsarki. Wasu harsunan suna kiran tsaunin da bishiyar Zaitun.
Tsaunin Zaitun a da
Shekaru 50 baya, yanayin ya sauya kwarai: fuskar katangar birnin da hasumiya su ne suke tabbatar da cewa wannan hoton da aka dauka a ranar 7 ga watan Junin 1967 shi ne na tsaunin Zaitun. A lokacin yakin kwanaki shida, wadannan sojoji suka yi mafka a wurin.
Masallacin Al-Aksa a yau
Masallacin Al-Aksa a tsohon Birnin Kudus shi ne masallaci na uku masu muhimmanci a Musulunci bayan masallatan Makka da Madina. Ga Yahudawa, wuri ne mai tsarki kamar yadda yake a koyarwar littafin Bible. Ana yawan rikici a kansa. Isra'ila ce ke kula da shi tun 1967, cibiya ce ga Musulmi ta al’amuran addini.
Masallacin Al-Aksa a da
Al-Aksa shi ne masallaci mafi girma a birnin. An kammala gininsa a farkon karni na 8. Yankin baki daya yana kewaye da kananan gine-gine masu tsarki. Ana danganta lambuna da idon ruwa da korama a Musulunci. Cikin masallacin na da sahu bakwai da ke iya daukar masallata 4,000.
Kofar Damascus a yau
Wannan kawatacciyar kofar ta Birnin Kudus tana iyaka tsakanin unguwannin Kiristoci da Larabawa. Wadanda ke wucewa ta kofar suna tafiya ta zirin hanya cikin tsari da nishadi ta Larabawa. Sai dai kofar ta arewacin tsohon Birnin na Kudus ya yi kaurin suna. Kofar Damascus ta kasance wurin da tsawon shekaru ake samun zubar da jinin Falasdinawa.
Kofar Damascus a da
An yi wa kofar lakabi da Damascus saboda hanyar ta dangana da Siriya, ita ce kofa mafi tsufa a katangar ta daular Ottomaniyya a karni na 16. Abubuwa da dama sun sauya in banda motoci da yawan jama’a a wajen katangar tun da aka dauki wannan hoto a watan Yulin 1967.
Tsohon garin a yau
Sarkakiyar hanyoyi sun hade yankunan Yahudawa da na Larabawa da Kiristoci da Armeniyawa a tsohon Birnin Kudus, kewaye da katanga da aka gina tsakanin 1535 da 1538 a karkashin jagorancin Annabi Sulaiman. A 1981, UNESCO ta sanya tsohon garin mai kwatankacin murabba'in kilomita daya cikin wurare masu tarihi na duniya.
Tsohon garin a da
Wasu abubuwan ba su sauya ba duk da shekaru 50 bayan da aka dauki wannan hoton a 1967, har yanzu yara suna yawo a kan tituna da sayar da kantu da mutanen yankin suke kira “Bagel” a kan Euro daya.
Katangar kunci a yau
Katangar mai tarihi a duniya ita ce babban wurin ibadar Yahudawa. Ana gudanar da ibada ce a nan da cikakken tsaro. Mutane na lika takardar addu’a ko bukatarsu a jikin bangon. Ana kuma iya yin hakan ma ta Internet ana wallafa addu’o'in da kuma fata a Birnin Kudus a lika a jikin katangar.
Katangar kunci a da
Hotunan da aka dauka a ranar 1 ga watan Satumba 1967 sun nuna 'yan Isra'ila a katangar yamma. A wancan lokaci babu shamaki zuwa katangar bayan kasancewa karkashin Jordan tsawon shekaru 19.