1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin wztar

Abdourahamane Hassane
November 25, 2022

Rahotanni daga Ukraine na cewar kusan rabin mazauna birnin Kyiv har yanzu ba su da wutar lantarki, kwanaki biyu bayan harin da Rasha ta kai kan muhimman ababen more rayuwa.

https://p.dw.com/p/4K4Rh
Ukraine Kiew | Dunkle Straße nach Angriffen auf Stromversorgung und Infrastruktur
Hoto: Ed Ram/Getty Images

Magajin garin birnin Kyiv Vitali Klitschko ya ce kIshi uku na gidajen birnin sun kasance cikin duhu tun Alhamis. Sai dai ya ce kwararru na ci gaba da yin aiki domin daidaita al'amura. Kamfanonin samar da wutar lantarkin na ta kokarin samar da wutar ga duk masu amfani da ita, yayin da yanayin sanhin huturu ya kai kasa ga maki daya  a ma'aunin Celsius ga kuma ruwan sama.