A farkon badi za a gudanar da taron tallafa wa Siriya
November 16, 2015Talla
Shugabannin kasar Birtaniya da Jamus sun ce za su gudanar da wani taro a farkon shekara mai zuwa don tara kudin tallafi ga 'yan Siriya da yakin kasar ya daidaita, wadanda kuma ke cikin halin kuncin rayuwa. A lokacin da suke magana a gefen taron kungiyar kasashe masu tagomashin tattalin arziki na G-20 a kasar Turkiyya, kasashen Jamus da Birtaniya sun ce tallafin da ake samu daga kasashen duniya ya ragu matuka. Yakin basasar Siriya ya haddasa matsalar 'yan gudun hijira mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu. Miliyoyin 'yan kasar sun rasa muhallansu yayin da kimanin dubu 250 suka mutu a yakin tsakanin dakarun gwamnati da na kungiyoyin 'yan tawaye ciki har da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci a Iraki da Siriya.