1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsoratar game da rashin zuwan yara makaranta a Birtaniya

Zulaiha Abubakar
June 9, 2020

Gwamnati ta dakatar da shirin bude makarantun firamare domin yara su fara karatu, sabon umarnin na daga cikin canjin muradun da firaiminista Boris Johnson ke gabatarwa a wannan lokaci na annobar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3dXSO
Großbritannien Klassenzimmer in London Flüchtlingskinder
Hoto: Reuters/S. Plunkett

Tun da fari sai da gwamnati ta daukarwa iyayen yara alkawarin bude makarantun firamare a wannan lokaci bisa sharadin bayar da tazara tsakanin dalibai, batun da kungiyar malaman makaranta ta yi na'am da shi kodayake wasu daga cikin 'yan jam'iyyar firaiminista Johnson sun soki shirin bude makarantun.

 

A nasa bangaren shugaban kwamitin ilimi a Majalisar Dokokin kasar Robert Halfon tsoratarwa ya yi game da yadda wasu yara ke zuwa makaranta yayin da wasu suke zaune a gida ba sa samun damar daukar darasi ta kafar Internet saboda iyayensu masu karamin karfi ne. Yanzu haka dai kididdigar da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar ta bayyana kusan mutane dubu 52 ne suka rasa rayuka sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.