Bakin haure daga Birtaniya zuwa Ruwanda
June 14, 2022Sakatariyar harkokin waje Liz Truss ta jaddada cewar jirgin farko zuwa Kigali wanda aka dauko hayarsa daga Spain zai tashi cikin dare, ba tare da la'akari da kankantar masu neman mafakar siyasar ba. Ya zuwa yanzu dai mutane bakwai ne kadai za a kai Ruwandan, maimakon 130 da aka ayyana tun farko saboda rashin kammala shari'ar kalubalantar fitar da su daga Ingila. Akwai dai alkaluma da ke nuni da bakin haure masu dimbin yawa da suka shiga Birtaniyan ta cikin ruwa daga yankin arewacin Faransa, lamarin da ya jefa gwamnati a London cikin yanayi na matsin lamba. Wannan batu dai ya tilasta mata daukar mataki, ba ya ga alkawarinta na sake tsananta tsaro a kan iyakokinta bayan ficewarta daga kungiyar Tarayyar Turai EU.
An kiyasta cewa sama da mutane dubu 10 ne suka cimma nasarar shiga Birtaniyan cikin kwale-kwale, a wannan shekara da muke ciki kadai. Ita kuwa gwamnatin Ruwanda mai masaukin baki, ta sake kare kanta ne dangane da wannan shiri mai sarkakiya na karbar masu neman mafakar siyasar da aka kora daga Birtaniya. Mahukuntan na KIgali, sun ce a shirye suke tsab, domin yin maraba ga dubban masu neman mafakar da hannu biyu. Birtaniyan dai ta cimma yarjejeniyar dalar Amirka miliyan 148 da Kigali, domin tura mata bakin haren masu neman mafakar siyasar da suka shiga kasar ta barauniyar hanya a kananan kwale-kwale daga wasu kasashen Turai. Majalisar Dinkin Duniya da ma kungiyoyin kare hakkin dan Adam dai sun nuna adawa da wannan yarjejeniya, sai dai mai magana da yawun gwamnatin Kigali Yolande Makolo ta bayyana ta da "shiri mai muhimmanci da aka kirkira".