Birtaniya ta kira taro kan Iran
July 22, 2019Talla
A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai Iran ta kame tankar man Britaniyan a mashigin ruwan Hormuz. An yi ta kace-nace ba tare da an samar da maslaha ba. Ko a ranar Lahadin da ta gabata, Ministan harkokin wajen kasar ta Birtaniya Jeremy Hunt, ya bayyana takaici kan matakin da gwamnatin Teheran ta dauka na nuna halin ko in kula a shawo kan wannan rikicin da ke son janyo wa kasashen biyu tsamin dangantaka. Saboda haka ne Firaministar Birtaniya Theresa May ta kira wani taron gaggawa da ya hada kan manyan jami'an gwamnati dana tsaro, kan takaddamar da ta kunno kai bayan da Iran ta kama tankar man kasar.