1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIngila

Sarki Charles na III ya amince da Starmer

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 5, 2024

Sarki Charles na III na Ingila ya rantsar da Keir Starmer na jam'iyyar Labour, a matsayin firaministan Birtaniya a hukumance a fadar Buckingham.

https://p.dw.com/p/4hw5m
Birtaniya | Keir Starmer | Sarki Charles na III
Sarki Charles na III tare da sabon firaministan Birtaniya Keir StarmerHoto: Yui Mok/AP Photo/picture alliance

Hotunan da suka bayyana daga fadar ta Buckingham dai, sun nuna Sarki Charles na musabaha da Firaminista Keir Starmer da jam'iyyarsa ta Labour ta samu nasara da dan karamin rinjaye. Daga bisani Keir Starmer ya isa fadar gwamnati ta Downing Street a karon farko a matsayin firaminista, tare da mai dakinsa Victoria Starmer jim kadan bayan ya gana da Sarki Charles na III. Tun da fari dai Rishi Sunak yya mika takardar murabus dinsa ga Sarki Charls na III sakamakon kayen da jam'iyyarsa ta Conservatives ta sha, a zaben da ya gudana bayan shekaru 14 tana kan karagar mulki.