1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar sabuwar yarjejeniyar nukiliya

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 23, 2019

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bukaci Amirka da kawayenta su samar da hanyar cimma sabuwar yarjejeniyar nukilya da kasar Iran, wadda za ta maye gurbin ta yanzu da ke tangal-tangal.

https://p.dw.com/p/3Q7U2
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Shugaban Amirka Donald Trump da na Iran Hassan RohaniHoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Firaminista Boris Johnson ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a gaban taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi da ke gudana a yanzu haka a birnin New York na Amirka, inda ya ce kamata ya yi amirka ta ajiye duk wani suka da  ta ke yiwa yarjejeniyar nukilyair da suka cimma da Iran a baya, domin lokaci ya yi da za a cimma wata sabuwar yarjejeniya. Koda yake ofishin firaministan na Birtaniya ya nunar da cewa har yanzu kasar na mutunta yarjejeniyar da suka cimma ta 2015, sai dai akwai bukatar ita ma Irna ta koma kan wannan yarjejeniya.

Da yake mayar da martani kan batun na Firaminista Johnson Shugaba Donald Trump na Amirka, ya yaba da matakin yana mai cewa yana girmama Johnson da tunaninsa. Amirkan dai ta fice daga yarjejeniyar a shekarar da ta gabata, tare da sake kakabawa Iran din sababbin takunkuman karya tattalin arziki, wanda na baya-bayan nan shi ne wanda ta kakabawa babban bankin Iran din, abin da ya sanya Tehran din cewa Amirkan ta toshe duk wata kafa ta zama kan teburin sulhu da kasar. Ministan  harkokin kasashen ketare na Iran din Mohammad Javad Zarif ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi. Johnson dai na son ganawa da Shugaba Donald Trump na Amirka da kuma takwaransa na Iran Hassan Rouhani a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi, kamar yadda shugaban Faransa Emmanuel Macron shi ma ke son ganawa da shugabannin kasashen biyu da ke wa juna kallon hadarin kaji, da nufin sulhunta su.