1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta ce mutanenta su fice daga Tunusiya

Yusuf BalaJuly 10, 2015

Ofishin harkokin wajen Birtaniya ya ce yana da yakinin cewa mahukuntan Tunusiya basu yi wani tanadi na bada kariya ga bakin da ke zuwa yawon bude idanu a kasar ba

https://p.dw.com/p/1Fw7L
David Cameron Premierminister Großbritannien
David Cameron Firayim Ministan BirtaniyaHoto: Reuters/A. Winning

Gwamnatin kasar Birtaniya ta bada umarni ga al'ummarta da ke zuwa yawon bude idanu a kasar Tunusiya da su fice daga kasar, inda ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar karin wasu hare-hare na 'yan ta'adda.

Ofishin harkokin kasashen wajen Birtaniya ya ce duk da cewa babu wasu shedu da ya tattara da suka tabbatar da wani yunkurin kai hari, yana da yakinin cewa mahukuntan wannan kasa da ke a Arewacin Afrika ba su yi wani tanadi ba na bada kariya irin wacce ta dace ga bakin da suke zuwa kasar dan yawon bude idanu.

Masu yawon bude idanu 38 ne dai aka kashe a wannan kasa, 30 daga cikinsu 'yan asalin Birtaniya bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wajen shakatawa na bakin ruwa ranar 26 ga watan Yuni a garin Sousse.

Bayan dai wannan farmaki a kasar ta Tunusiya gwamnati ta sanya dokar tabaci, kana ta kara tsaurara matakan tsaro a wuraren da baki 'yan kasashen waje ke zuwa a kasar.