Birtaniya ta koka a kan yawan al'ummar da ke cirani a kasar
May 25, 2023Talla
A shekarar 2022 mutum milyan 1,200 ne suka shiga kasar amma wadanda suka fice da kadan suka haura mutum dubu dari biyar.
Ana alakanta wannan wannan tururuwa da kasar ke fuskanta a yanzu haka da da riringimun da duniya ke ciki, kama daga yakin Rasha da Ukraine da murkushe 'yan yankin Hong Kong da mahukuntan China ke yi da ma janye dokokin corona da aka yi.
Lamarin da ya kai muahukuntan kasar daukar tsauraran matakai ciki harda haramtawa daliban kasashen waje kai iyalansu kasar da nufin rage yawan 'yan cirani da ke shiga kasar.
Wannan sabuwar doka dai za ta shafi daliban ne da ke karatun digiri na daya da na biyu. Firanministan Birtaniya Rishi Sunak ya ce wannan matakin zai taimaka matuka wajen rage yawan jama'a da ke shiga kasar.