1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta tuhumi matasa da ta'addanci

Yusuf BalaJuly 21, 2015

Matasan na Birtaniya dai an tuhumesu ne da wani shiri na shiga kungiyar masu tada kayar baya da ke ayyukan rashin imani a kasashen Siriya da kuma Iraki.

https://p.dw.com/p/1G2C9
Nach Terroranschag in London Durchsuchung in Leeds
Jami'ai da binciken ayyukan masu tada kayar bayaHoto: AP

Masu gabatar da kara a Birtaniya sun tuhumi wasu mutane biyu da laifin yunkurin shiga kungiyar mayakan IS a Siriya. Cibiyar masu shigar da karar ta Birtaniya ta bayyana cewa Junead Ahmed Khan dan shekaru 24 da dan uwansa Shazib Ahmed Khan me shekaru 22 an tuhumesu da yunkurin shiga kungiyar ta'addanci.

A makon jiya ne dai aka kama wadannan matasa a garin Luton da ke arewacin birnin London. Mutum na uku da ake zargi da alaka da ta'addancin wanda kuma aka kamasu tare an sallameshi ba tare da wata tuhuma ba.

Mahukunta dai a Birtaniya sun bayyana cewa kimanin 'yan Birtaniya 700 ne suka fice daga kasar zuwa Siriya dan tallafawa ayyukan masu tada kayar baya.