Birtaniya za ta kori baki zuwa Ruwanda
April 15, 2022Talla
Shugaban gwamnatin na Birtaniya Boris Johnson da ke yin jawabi a garin Kent da ke kudu maso gabashin kasar, ya ce duk wadanda suka shiga Birtaniya ba bisa ka'ida ba tun daga farkon watan Janairu dama wadanda ke zaune a kasar da dadewa za a tisa keyarsu zuwa Ruwanda. MDD da kungiyar kare hakin bil Adama ta Amnesty international sun yi Allah wadai da matakin da suka kira koma bayan a kan sha'anin kare hakkin dan Adam.