1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Limaman Coci za su bar aiki a Chile

Abdul-raheem Hassan
May 18, 2018

Zargin yawaita cin zarafi da lalata, ya tilasta dukkannin limaman Coci mika takardun barin aiki ga shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis.

https://p.dw.com/p/2xxY2
USA - Gottesdienst - Priester
Hoto: imago/UPI Photo

Dukkannin manyan limaman cocin kasar Chile 34, sun mika takardaun ajiye aiki ga shugaban darikar katolika na duniya Paparoma Francis, bisa zargin lalata da cin zarfi a fadin kasar.

Ganawar paparoman da limaman Cocin ya biyo bayan binciken fadar Vatican ta yi kan rufa-rufa a kan aikata lalata da cin zarafi a kasar, ciki har da nadin da Paparoman ya yi wa Boshop Juang Barros a 2015 duk da zargin lalata da ake a kanshi.

A wata sanarwa da limaman Cocin suka fitar, sun nemi afuwar 'yan kasar da kuma iyalan wadanda abin ya shafa tare da cewa suna jiran matakin da Paparoman zai yanke kan bukatun ajiyae aikin.