1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blinken ya gana da Mahmud Abbas

Zainab Mohammed Abubakar
January 31, 2023

A ganawarsa da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, sakataren harkokin wajen Amurka ya nuna alhini a kan asarar rayuka da aka yi a sabon rikicin da ya barke a yankin.

https://p.dw.com/p/4MvxB
Palästinensische Autonomiegebiete | Besuch Antony Blinken in Ramallah
Hoto: Ronaldo Schemidt/AFP/Getty Images

Babban jami'in diflomasiyyar na Washington ya gana da Abbas a birnin Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan a karshen ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya da nufin dakile zubar da jinin da ake yi, bayan ganawar da ya yi da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan harkokin wajen kasar.

 Bangarorin biyu dai na cikin rudani na sabon tashin hankali. Wani Bafalasdine ya bindige mutane 7 a wani matsugunin Isra'ila da ke gabashin birnin Kudus a ranar Juma'a, kwana guda bayan harin da sojojin Baniyadun suka kai mafi muni cikin shekaru, a Yammacin Gabar Kogin Jordan, da ya lashe rayukan Falasdinawa 10.

 A wannan watan rikicin ya yi sanadin mutuwar manya da kananan yara Falasdinawa 35, da suka hada da maharan, da kuma fararen hular Isra'ila shida da suka hada da karamin yaro da dan kasar Ukraine daya da aka kashe a ranar Juma'a.