Nijar: Hare-hare na kamari a Diffa
May 11, 2020Kusan karo uku ke nan cikin kwanaki biyar, mayakan na Boko Haram na kai hari kusa da birnin na Diffa, duk kuwa da cewa jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar na rike da wajen. Yankin dai na da nisan kilo mita uku da birnin na Diffa, a kan iyakar Jamhuriyar ta Nijar da makwabciyarta Tarayyar Najeriya, da ke zaman makyankyasar Boko Haram din. Wadannan hare-hare dai, sun tayarwa da al'umma hankali.
Rahotanni sun nunar da cewa ko a shekara ta 2015 da mayakan na Boko Haram din suka zafafa hare-hare, sun sha kai hare-hare a yankin sai dai ba su samu nasara ba. A cewar Marah Mamadu na kungiyar Alternative, tilas kasashen da wannan abu ya shafa su hada ahnnu wajen magance matsalar tsaron, domin yakin ba na kasa guda ba ne.
A ranar Lahadin da ta gabata dai, shugabannin rundunonin tsaron Jamhuriyar ta Nijar baki daya, sun fantsama cikin daji da nufin farauto maharan na Boko Haram a duk inda suke. Wannan matakin nasu dai ya farantawa wasu mazauna yankin rai, inda har ma suke taya sojojin ta addu'o'in samun nasara.