Griechenland Generalstreik
May 5, 2010Yanzu haka dai yajin aiki da zanga zangar da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi a ƙasar Girka ya fara ɗaukar wani sabon salo, kana yana ƙara durƙusar da ƙasar wadda a yanzu haka ta ke cikin tsaka mai wuya, bisa basukkan da suka yi mata katutu. Usman Shehu Usman ya duba mana halinda ake ciki a ƙasar.
Ƙasashen dake amfani da kuɗin Euro sun yi gargaɗin cewa halin da ƙasar Girka ke ciki yana iya yaɗuwa. Sun yi wannan maganar bayan da a yau zanga- zangar da 'yan ƙasar ta Girka masu adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati ya nemi rikiɗewa zuwa wata tarzoma. A yau ɗin dai aƙalla mutane shidda suka rasa rayukansu wasu da dama suka jikkata, yayin da masu boren suka cinnawa wani banki wuta.
Da take magana da 'yan majalisar dokoki na Budestag, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bayyana cewa wannan lamarin idan ya yi ƙamari, bawai Girka ce kaɗai za ta ji a jika ba:
Merkel ta ce, lamarin fa bawai ƙarami bane da zai shafi makomar Jamus kaɗai ba. Amma abune da zai shafi makomar Jamus ne da nahiyar Turai.
Yanzu haka dai batun bashin dake kan ƙasar Girka, ya kusa taɓo dukkan duniya domin faɗuwar darajar kuɗin Euro ya sa kasuwannin a Turai da Asiya dama Amirka duk sun faɗi.
Idan mutum ya duba lamarin a cikin gidan ƙasar ta Girka wanda take samun ɗimbin kuɗi ta baƙi masu yawon shaƙatawa to dole sai ya tausaya. Kamar yadda wannan ɗan ƙasar mai sana'ar kawo baƙi masu yawon shaƙatawa ya ke cewa:
Mun fara ɗanɗana masifar da ƙasarmu ta shiga. A ɗan ƙaramin lokaci bama iya fahintar yadda makomar ƙasar mu za ta kansance. Sai dai kawai muna fata a wannan ranin za a samu sa'ida
A yau dai ko da kafafen yaɗa labarai basa aiki, don haka babu radeyo da talabijin in banda kafen yaɗa labarai na gwamnati da kuma wani gidan jarida ɗaya, wanda ma'aikatanta suka buga labarai a yanar gizo kawai don sanar da mutuwar mutanen da aka yi. An dai yi ƙiyasin kimanin mutane dubu 100, suka shiga zanga zangar cikin yajin aikin gama gari na sa'o'i 24 a faɗin ƙasar.
Wannan rigimar ta shafi ƙasashen kudancin Turai da dama. Misali yan ƙasar Bulgeriya kimanin dubu 100 ke aiki a ƙasar Girka, haka ƙasar Macedoniya akwai bankunan Girka da dama waɗanda suka zuba jari a ciki. Ga dai abinda Starevsk ministan kuɗi na ƙasar Macedoniya yake cewa:
Alamun tashin hankali da yajin aiki a Girka zai shafi ƙasar mu. Amma bana jin bakunan ƙasar Girka dama na ƙasashe maƙobta za su janye kuɗinsu. Misali ma ´aikaci a nan Macedoniya yana samun Euro ɗari a wata guda. Amma a Girka ba haka bane.
Yanzu haka dai ƙasashen Rumeniya da Bulgeriya sun shiga cikin zullumi. Domin suna gudun kada ƙasashen da ake amfani da Euro su ɗau wasu matakai a kansu, sakamakon darasin da aka ga a ƙasar Girka, inda yanzu komai ya tsaya cik.
Mawallafa: Jannis Papadimitriou da Usman Shehu Usman
Edita:- Ahmadu Tijjani Lawal