1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bore da yajin aiki a ƙasar Girka

Usman ShehuSeptember 26, 2012

A ƙasar Girka yajin aiki da zanga zangar jama'a ya rikiɗe izuwa tarzuma

https://p.dw.com/p/16FHS
A molotov cocktail explodes beside riot police officers near Syntagma square during a 24-hour labour strike in Athens September 26, 2012. Flights and trains were suspended, shops pulled down their shutters and hospitals worked on emergency staff on Wednesday in Greece's first big anti-austerity strike since a coalition government took power in June. REUTERS/Yannis Behrakis (GREECE - Tags: BUSINESS CIVIL UNREST POLITICS)
Yan sanda da masu bore a GirkaHoto: Reuters

Yan sanda a birnin Athens na ƙasar Girka suna can suna karawa da masu bore, masu boren dai suna adawane da shirin tsuke bakin ajihu gwamnati, inda suke amfani da kwalabe da bama bamai haɗin gida, inda suke taho mugama da yan sanda. Yan sanda su kuwa suna mayar da martani da fesa hayaƙi mai sa kwalla, abinda kuma ya sa boren na yau ya rikiɗe izuwa wata babbar tazuma. Aƙalla mutane dubu 50 suka shiga boren wanda kungiyoyin ƙwadogo suka ƙira a yi. Yajinn aikin da aka shiga a ƙasar dai ya sa an rufe makarantu, kana ya katse zirga-zirgar jiragen sama.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu