Boren ƙungiyoyin ƙwadagon Spain
July 20, 2012Ɗarurawan 'yan Spain waɗanda suka fusata kan matakan tsuke bakin aljihun ƙasar sun gudanar da zanga-zanga a manyan biranen ƙasar na Madrid Barcelona da Sevilla a daidai lokacin da ministocin kudin turan ke shirin ganawa ta wayar tarho a wannan juma'ar, dangane da shirinsu na ceto ƙasar.
A madrid masu zanga-zangar da suka haɗa da 'yan kwan-kwana, da mallaman makaranta da ma ma'aikatan gwamnati sun zargi gwamnatin masu ra'ayin ruiƙau na Frime Minista Marianno Rajoy da gudanar da gwamnatin fashi da makami.
A makon da ya gabata ne Frime MInista Rajoy ya sanar cewa za'a cire garaɓasar da ma'aikatan kan samu lokacin sallar Krisimati a kan wani albashin da aka dorawa hannu a shekarar 2010 a kuma ƙara kuɗin haraji kan.
Ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun ce a tsukin shekaru huɗu kawai zasu rasa kimanin kaso 15 na kuɗaɗensu.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala