1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da fyade a Pakistan

September 15, 2013

Masu fafutuka sun shirya gangamin yin Allah wadai da fyaden da a ka yiwa wata 'yar shekaru 5 a Pakistan.

https://p.dw.com/p/19hxS
Pakistani supporters of WAPDA Hydro Electric Central Labour Union chant slogans during a protest against inflation in Lahore on July 27, 2011. Pakistan's economy had grown only 2.4 percent in the fiscal year ending June 30 with the fiscal deficit at 5.3 percent of GDP and inflation at 12 percent. AFP PHOTO/ARIF ALI (Photo credit should read Arif Ali/AFP/Getty Images)
Hoto: Arif Ali/AFP/Getty Images

Masu fafutukar kare hakin jama'a a Pakistan, sun gudanar da jerin gwanon yin tofin Allah tsine a sassa daban daban na kasar, domin nuna adawarsu a kan fyaden da a ka yi wa wata yarinya 'yar shekaru biyar a birnin Lahore, da ke gabashin kasar, birnin da kuma a ke samun zaman lafiya sosai, idan a ka kwatanta da sauran yankunan kasar.

Wani jami'in tsaron kasar, ya bayyana cewar, ya zuwa yanzu dai, jami'an 'yan sanda ba su da wani bayani dangane da mutumin da ya tafka wannan aika-aikar, duk kuwa da cewar, sun tsare mutane da dama da suke zargi, tare da sakinsu bayan yi musu tambayoyi. Idan za a iya tunawa dai, tun a ranar Alhamis (12. 09. 13) da ta gabata ce, a ka sace yarinyar, tare da yi mata mummunan fyade.

'Yan sandan sun kara da cewar, a ranar Jumma'a ce (13. 09. 13) a ka gano yarinyar kusa da wani asibiti, yini daya bayan saceta. Wani jami'in kula da lafiya a asibitin, Dakta Farzand Ali, ya ce ko da shike tana wurin da a ke kula da masu fama da rashin lafiya mai tsanani, amma tana samun ci gaba, sakamakon irin kulawar da take samu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu