Faransa: Adawa da karin harajin fatur
December 1, 2018Talla
Hukumomi sun rufe tashoshin jiragen kasa 19 sakamakon barkewar arangama tsakanin 'yan sanda da masu nuna fushi da karin haraji kan man fetur. An tsare mutane 160 daga cikin masu zanga-zanagar, 'yan sanda 11 sun jikkata.
An kiyasta mutane dubu 5,500 ne suka gudanar da jerin gwano a babban birnin kasar Paris, yayin da wasu dubu 36, suka gudanar da zanga-zanagar a sauran sassan kasar.
Karin haraji kan man fetur da Shugaba Emmanuel Macron ya yi na da nasaba da yunkurin rage amfani da motoci masu fitar da hayaki, sai dai 'yan fafutuka na kalubalantar shugaban da rashin la'akari da tsadar rayuwa da ake fama.