1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan DR Congo sun yi tir da Ruwanda kan M23

Abdul-raheem Hassan
June 15, 2022

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, domin nuna adawa da kasar Rwanda kan nanata ikirarin goyon bayan ga kungiyar 'yan tawayen M23.

https://p.dw.com/p/4CkxQ
Kwango Goma |
Hoto: Moses Sawasawa/AP/picture alliance

An samu tashin hankali a birnin da ke kan iyaka, yayin da ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka tarwatsa wasu masu zanga-zangar, yawancinsu fusatattun matasa sun ciccire kayansu, sun kuma yi yunkurin kutsawa bakin iyakar kasar da Rwanda, kamar yadda wani wakilin AFP ya gani.

An rufe bankuna da gidajen mai da makarantu da shaguna da sauran kantuna a fadin garin na Goma, rahotanni na cewa an samu jikkatar mutum guda a hatsaniyar, Jama'ar sun yi ta rera taken nuna adawa da Rwanda da shugabanta Paul Kagame.

A cikin 'yan makwannin da suka gabata an yi takun-saka tsakanin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) da makwabciyarta gabacinta kan 'yan tawayen M23.