1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren ƙungiyoyin ƙwadagon Spain

July 20, 2012

Al'ummar Spain na gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sabbin matakan tsuke aljihun da ke barazanar rage kuɗaɗen albashinsu da kusan kashi 15 cikin 100

https://p.dw.com/p/15bm8
Demonstrators rise their hands as they shout slogans during a protest at Sol square, in Madrid, Friday May 20, 2011. Spanish university students and youth groups are protesting against a youth unemployment rate of 40 percent and austerity measures taken to end Spain's debt crisis. (Foto:Emilio Morenatti/AP/dapd)
Hoto: dapd

Ɗarurawan 'yan Spain waɗanda suka fusata kan matakan tsuke bakin aljihun ƙasar sun gudanar da zanga-zanga a manyan biranen ƙasar na Madrid Barcelona da Sevilla a daidai lokacin da ministocin kudin turan ke shirin ganawa ta wayar tarho a wannan juma'ar, dangane da shirinsu na ceto ƙasar.

A madrid masu zanga-zangar da suka haɗa da 'yan kwan-kwana, da mallaman makaranta da ma ma'aikatan gwamnati sun zargi gwamnatin masu ra'ayin ruiƙau na Frime Minista Marianno Rajoy da gudanar da gwamnatin fashi da makami.

A makon da ya gabata ne Frime MInista Rajoy ya sanar cewa za'a cire garaɓasar da ma'aikatan kan samu lokacin sallar Krisimati a kan wani albashin da aka dorawa hannu a shekarar 2010 a kuma ƙara kuɗin haraji kan.

Ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun ce a tsukin shekaru huɗu kawai zasu rasa kimanin kaso 15 na kuɗaɗensu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala