1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Botswana: Masisi ya zama shugaban kasa

Yusuf Bala Nayaya
April 1, 2018

Sabon shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi yayi amfani da lokacin rantsuwar kama aiki a ranar Lahadi wajen shan alwashi na tunkarar matsalar aikin yi a tsakanin matasa a kasar da ba ta fuskantar tashin-tashina.

https://p.dw.com/p/2vLBF
Botswana Vize-Präsident Mokgweetsi Masisi
Hoto: Imago/Xinhua

Sabon shugaban yayi rantsuwar kama aikin ne bayan da Shugaba Ian Khama ya kammala shekaru 10 da tsarin mulkin kasar ya tanadar masa abin da ya sa ya sauka. Mataimakinsa Masisi ya hau kujerar ba tare da wata matsala ba kuma alamu sun nunar da cewa zai samu wa'adi na shekaru biyar nan gaba idan aka yi zabe a watan Oktoba na shekara mai zuwa inda ake sa ran jam'iyya mai mulki ta BDP za ta ci gaba da zama a madafun iko.

Kasar ta Botswana na alfahari da shugabanci na gari da bin doka da oda, kuma an mika mulkin ne ga sabon shugaban cikin tsanaki watanni 18 kafin zaben 'yan majalisa a 2019. Kasar na da labari mai kyau inda take amfani da damarta ta albarkatun deman da naman shanu da bunkasar yawan bude ido.