Bouteflika ya sake lashe zaben Aljeriya
April 18, 2014Sakamakon farko na zaben shugaban kasar da ya gudana a kasar Algeriya, ya bayyana Abdelaziz Bouteflika, a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 81,53% na kuri'un da aka kada. Abokin hamayyar sa Ali Benfils ya zo a matsaiy na biyu inda ya samu kashi 12,18%. Sai kuma Abdelaziz Belaïd da ya samu kashi 3,36%. Snnan Louisa Hanoune ta samu kashi 1,3%.
An kiyasta adadin wadanda suka fito suka yi zaben a matsayin kashi 51,7% na wadanda suka yi rejista, duk kuwa da kiran da 'yan adawan kasar suka yi na a kauracewa zaben. Da ma dai tun kafin zaben, ake ikirarin cewa Shugaba Bouteflika ne zai lashe zaben, a gaban yan adawar kasar da ke da rabuwar kawuna. Da farko dai dan takara Ali Benfils, yayi watsi da sakamakon inda ya ce an tafka babban magudi a cikinsa.
Shugaba Bouteflika dai dan shekaru 77 da haihuwa, ya kwashe a kalla shekaru 15 a kan karagar mulkin kasar ta Aljeriya, inda a halin yanzu ya samu wani sabon wa'adi na hudu. Sai dai kuma sakamakon na wannan lokaci, bai kai ga na shekarar 2009 inda ya samu kashi 90% na kuri'un da aka kada.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe