1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bolsonaro na Brazil ya yi watsi da dokar Corona

Gazali Abdou Tasawa
July 4, 2020

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya yi amfani da karfin da doka ta ba shi wajen hana aiki da wasu matakan yaki da annobar Covid 19 da majalisar dokokin kasar ta dauka.

https://p.dw.com/p/3enX3
Brasilien | Coronavirus | Jair Bolsonaro
Hoto: picture-alliance/dpa/Palacio Planalto/M. Correa

Majalisar dokokin kasar dai ta amince da wasu dokoki ne guda biyu wadanda suka tilasta wa jam'a sanya takunkumi a wuraren taruwar jama'a da a shaguna da kuma Coci, da kuma tarar kudi ga wadanda suka ki mutunta su.

Dokokin da Shugaba Bolsonaro ya hau kujerar naki kan amfani da su yana mai cewa sun saba dokar tsarin mulkin kasar wacce ta ke ba da kariya ga siirukan rayuwar dan Adam. Majalisar dokokin kasar ta Brazil dai na da kwanaki 30 domin cilasta amfani da dokokin na Corona ko kuma yin watsi da su.