1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil ta haramta wa Bolsonaro zuwa bikin rantsar da Trump

Zainab Mohammed Abubakar
January 16, 2025

Kotun kolin Brazil ta ki amince wa rokon da tsohon shugaba Jair Bolsonaro ya yi, na mayar masa fasto dinsa don halartar bikin rantsar da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump a birnin Washington.

https://p.dw.com/p/4pFO8
Tshohon shugaban Brazil Jair BolsonaroHoto: Amanda Perobelli/REUTERS

Mai shari'a Alexandre de Moraes da Bolsonaro ke gani a matsayin abokin adawarsa, ya shaida cewar, tsohon shugaban ba shi da wani hurumin wakiltar Brazil a ko'ina, bugu da kari bai ma gabatarwa kotu shaidar da ke tabbatar da cewa an gayyace shi bikin rantsuwar ba.

Rundunar 'yan sandan kasar ce ta kwace masa fasfo a cikin watan Fabarairun bara, bisa tarin zarge-zargen da ake masa na aikata laifuka, ciki har da kin barin kujerar shugabancin Brazil, duk kuwa da shan kayen zabe da ya yi a hannun Luiz Inácio Lula da Silva.

Tun farko dai Bolsonaro, ya roki kotun da ta bada umarnin mayar masa da fasfo domin yin bulagaro a gobe Juma'a 17 ga watan Janairu, sannan ya koma gida ranar 22 ga watan.