1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArgentina

Ajantina ta ce ba za ta shiga BRICS ba

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 29, 2023

A wani abu da ka iya zama koma-baya ga kungiyar Kasashe da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa Cikin Sauri wato BRICS, shugaban kasar Ajantina Javier Milei ya ki amincewa da shiga cikinta a hukumance.

https://p.dw.com/p/4aidF
Ajantina | Javier Milei | Watsi | BRICS
Shugaban kasar Ajantina Javier MileiHoto: Agustin Marcarian/REUTERS

Fadar shugaban kasar Ajantina Javier Milei ce ta sanar da cewa, Shugaba Milei ya aike wa kungiyar ta BRICS takardar kin amincewa da shiga cikin nata. A watan Agustan wannan shekara ne dai kungiyar ta BRICS da ta kunshi kasashen Brazil da Rasha da Indiya da Chaina da kuma Afirka ta Kudu ta yanke shawarar karbar karin kasashe shida a cikinta, domin yin gogayya da kungiyar Kasashe ma su Karfin Arzikin Masana'antu na Duniya. Bayan kammala taron nata na watan Agusta, kungiyar ta BRICS ta sanar da yin maraba da kasashen Ajantina da Habasha da Iran da Saudiyya da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da ake sa ran za su zama cikakkun mambobinta daga ranar daya ga watan Janairun shekara ta 2024 mai kamawa.